
Rundunar ƴansanda ta jihar Katsina, a yau Lahadi, ta yi alkawarin ba da tukuicin Naira miliyan 50 ga duk wanda ya samu bayanai masu amfani da za su kai ga cafke yan bindiga biyu – Modi Modi da Jan Kare.
Rundunar, a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na jihar, Abubakar Aliyu, ya fitar, ta yi zargin cewa ƴan bindigar ne ke da alhakin yawancin hare-haren ta’addanci a jihar.
Sanarwar ta yi zargin cewa Modi Modi da Jan Kare, dukkansu maza, suna gudanar da ayyukansu a cikin jihar Katsina, musamman a yankunan kananan hukumomin Kankara da Safana.
“Tsaron mazauna yankin yana da matukar muhimmanci, shi ya sa muke yin wadannan alkawurran. Muna daukar kwararan matakai kan masu aikata laifuka da ke barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali,” inji shi.
Aliyu ya bayyana cewa za a ɓoye bayanan duk wanda ya kawo bayanin inda su ke, inda ya kara da cewa za kuma a ɓoye bayanan da aka bayar.
“Ana kira ga dukkan al’umma da abin ya shafa da su ba mu duk wani bayani da ya dace da zai taimaka wa jami’an tsaro wajen kamo masu shirya wadannan munanan laifuka na garkuwa da mutane da ‘yan fashi a jihar,” inji shi.
Ya kuma bukaci duk wanda yake da wani bayani da ya tuntubi hedkwatar rundunar ko kuma ya kira lambobin waya kamar haka: 07015142112 08023871144