Categories
Labarai

Rundunar sojan Najeriya ta sallami ‘yan Boko Haram 244 da aka sauyawa tunani

Rundunar sojan Najeriya a ranar litinin ta sallami wasu ‘yan Boko Haram 244 daga inda ake tsare da su, bayan an sauya musu tunani.

Rogers Nicholas, jagoran rundunar Lafiya Dole, shi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake mika mutanan da rundunar ta sallama zuwa hannun Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima a harabar rundunar sojan dake Maimalari, a birnin Maiduguri.

Mista Nicholas yace, mutanen da ake tsare da su, an sake su ne sabida sun sauya halinsu. Yace rundunar tayi hakan ne a cigaba da bukukuwan tunawa da tsaffin ‘yan mazan jiya.

Ya bayyana cewar, mutanan da aka saki sun kunshi maza 118 da kuma mata 56 da yara wada da basu balaga ba 19 da kananan yara 51.

Mista Nicholas yace “Shugaban rundunar sojan kasa ta Najeriya, Tukur Yusuf Buratai ne ya bayar da umarnin a saki mutanan, sabida sun sauya halinsu, sun koma mutane na gari”

“Mutanan dai anci nasarar sauya mutu tunani daga yaki zuwa zaman lafiya da kuma mayarda su su zama mutanan kirki wadan da al’umma zata amfana da su. Mun kuma hannanta su ga Gwamnatin jihar Borno”

Gwamnan Borno Kashim Shettima, ya jinjinawa rundunar sojan ta Najeriya, akan nasarar da suka samu na sauyawa mutanan tunani, kuma wannan shi ne hakikanin abinda ya dace inji shi.

Gwamnan ya kuma yi addua ga sojojin da suka rasa rayukansu a bakin daga,daga nan kuma yayi kira ga al’umma da su taimakawa iyalan sojojin da suka mutu a bakin daga, domin taimaka musu samun ingantacciyar rayuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *