Categories
Kanun Labarai

Rundunar sojin Najeriya ta ɓara, bayan da DAILY NIGERIAN ta bayar da labarin kisan gillar da wani soja ya yiwa wani Bahaushe me sana’ar fawa

Kaftin Maiwada Mohammed yace, rundunar sojon Najeriya ta ɓara sakamakon wani labari da wata kafaryada labarai ta intenet ta bayar kan kisan gillar da wani jami’in sojanta ya yiwa wani Bahaushe mai sana’ar fawa, dan yaki bayar da cin-hancin naira 500 a shingen jami’an tsaron binciken ababen hawa dake Uromi.

Rundunar Sojin Najeriya karkashin bataliya ta 4 dake birnin Benin, ta kafa wani kakkarfan kwamitin bincike, dan gano musabbanin kisan gillar da wani jami’inta mai suna Sunday ya yiwa wani Mahauci da ya dauko Shanu daga Arewa zuwa yankin kudancin Najeriya.

A ranar Alhamis, DAILY NIGERIAN HAUSA ta yi wani rahoto na musamman akan yadda wani Soja mai suna Sunday ya kashe wani mahauci mai suna Shaiu Garba kan yaki bayar da cin hancin Naira 500 a shingen Jami’an tsaron dake Uromi a jihar Edo.

A wani bayani da ta fitar ranar Asabar a birnin Benin wanda Kaftin Maiwada Mohammed ya sanyawa hannu, haka kuma, Maiwada shi ne mataimakin Daraktan sashin hulda da jama’a na rundunar sojin Najeriya dake Benin, ta bara kan wannan batu.

Maiwada yace, hankalin rundunar sojin Najeriya ya kai zuwa ga wani rahoto da wata kafar sadarwa a intanet ta yi na kisan wani mai sana’ar fawa wanda Bahaushe ne, mutumin ya rasa ransa a sakamakon harbin da wani soja yayi masa kan yaki biyar da cin-hancin Naira 500 a wani shingen jami’an tsaron soja dake Uromi a jihar Edo.

Yace, wannan al’amari ya auku ne, a wani shingen jami’an tsaron soja wanda yake karkashin bataliya ta 195 dake titin Agbor.

Ya cigaba da cewa, Sojan ya kashe mutumin ne, a sabida yaki bayar da cin-hancin da jami’an tsaron sojan suka nema a wajensa.

A cikin bayaninsa, yace, sojoji masu sintiri ne da suke binciken ababen hawa, suka bude wuta kan wata mota da ta nemi tsrewa, amma cikin tsautsayi sai harsashin ya samu shi wannan matukin motar da ya dauko shanu daga Arewa.

Wannan al’amari dai ya haifar da wata zazzafar zanga zanga daga masu tuka manyan motoci, wadan da suka toshe babbar hanyar shiga garin Benin a daidai shataletalen Ewu, wanda daga bisani suka janye ababen hawansu, aka cigaba da mu’amala kamar yadda aka saba.

Maiwada ya cigaba da cewar, bayan nuna alhini da juyayi da rundunar sojin Najeriya ta yi na rasuwar wannan bawan Allah Shafiu Garbaga iyalansa, yace kuma, rundunar ba zata lamunci irin wannan keta hakki da karya doka da wasu daga cikin jami’anta suke yi ba akan hanyoyin da aka turasu domin bayar da aminci da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya kuma tabbatar da cewar, tuni rundunar ta cafke shi wannan soja da yayi wannan mummunan aiki, kuma tuni aka kafa wani kakkarfan kwamitin bincike domin bincikar musabbabiyar faruwar lamarin.

“Ina son na tabbatarwa da al’umma cewar rundunar sojan Najeriya, zata cigaba da gudanar da ayyukanta tare da bin doka da oda da kuma kiyaye hakkin mutane musamman akan hanyoyi.”

“Muna kara sanarwa da dukkan masu amfani da manyan hanyoyi, da su samu nutsuwa akan jami’anmu, aikin rundunar sojojin Najeriya dake kan manyan hanyoyi shi ne samar da aminc akan hanyoyi, hakkinta ne ta amintar da dukkan matafiya, kuma kada mutane suji wata shakka ko kuma dar wajen bin doka akan hanyoyi, domin sojoji ba azzalumai bane, kuma za’a hukunta duk wani soja da aka samu da laifin cin zarafin mutane”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *