
Rundunar sojan saman Nijeriya ta ce ‘yan Nijeriya da suka cancanta zasu iya neman shiha aikin sojan sama na shekarar 2024.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar ta bakin Air vice marshal, Ahmed Bakari, ta ce masu neman aikin zasu cike fom ne a online sau 1 a yayin da za a soke cancantar wadanda suka cike sama da sau 1.
Bakari ya ce, za a fitar da fom din sheda na karamar hukuma dana amincewar iyaye da zarar an kammala cike neman aikin a shafin rundunar.
Ya ce dole ne takardun fom din su samu sanya hannun shugaban karamar hukuma ko jami’in soji.
“Masu neman aikin dole su kasance ‘yan Nijeriya kuma su zama suna da shedar NIN ko BVN”, inji sanarwar.
Haka kuma sanarwa ta ce masu neman aikin su kasance suna da isasshiyar lafiya kuma ba a taba samunsu da laifi ba
Haka kuma, masu son shiga aikin sojan, su zama suna shekaru 18 zuwa 22, haka kuma ya zama suna da Credit 5 a WAEC ko NECO .