23.1 C
Abuja
Tuesday, February 7, 2023

2023: Ba ruwanku da shiga harkokin siyasa, IGP ya gargaɗi ƴan sanda

Must read

Sufeto-Janar (IGP) na ƴan sandan Najeriya, Usman Baba, ya gargaɗi jami’an ƴan sandan Nijeriya da su guji shiga harkokin siyasa kafin, lokacin da kuma bayan zaɓen 2023.

IGP ya yi wannan gargadin ne a wata ziyara da ya kai hedikwatar ƴan sandan jihar Kogi da ke Lokoja a jiya Litinin.

Ya ce, “Bari in yi muku wani gargaɗi: kar ku shiga harkokin siyasa kafin zaɓe, da lokacin da kuma bayan zaɓe mai zuwa. Kada ku bari ƴan siyasa su yi amfani da ku domin za su juya baya ne bayan zabe.”

“Ku kawai aikin ku shi ne alhakin kiyaye kundin tsarin mulki da kare rayuka da dukiyoyin ƴan kasa; kuma ya zame muku dole ku sauke wannan nauyin.”

IGP ɗin ya kuma yi alkawarin duba kalubalen da ƴan sandan ke fuskanta, musamman masu ƙananan matsayi, da nufin samar da yanayi mai kyau domin karfafa musu gwiwa su yi aikin su yadda ya dace.

More articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Latest article

- Website Designed By DEBORIAN.COM, a Nigerian Web Designer and Web Developer -