Sabon Shugaban hukumar leken asiri ta kasa, Ahmed Rufai Abubakar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Ahmed Rufai Abubakar a matsayin Shugaban hukumar leken asiri ta Najeriya NIA.

A wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban kasa Femi Adesina ya sanyawa hannu, sanarwar ta ce, Sabon shugaban hukumar kwararren ma’aikacin Diplomasiiya ne. Kafin nadin nasa shi ne mai taimakawa Shugaban kasa na musamman akan harkokin kasashen waje.

“Ahmed Rufai Abubakar, tsohon ma’aikacin majalisar dinkin duniya ne akan harkokin zaman lafiya, da sasanta al’umma, sannan kuma kwararre ne ta fannin Diplomasiyya da hulda da kasashen waje, mutum ne mai kokarin bin doka da oda kiyaye ka’ida”

“Kafin Shugaban kasa ya nada shi a mukamin SSAP, ya rike mukamin mai bayar da shawara na musamman kan yadda za’a samar da zaman lafiya da fahimtar juna kan kasashen yankin tafkin Chadi”

“Ahmed Rufai, yana da digiri akan harshen Faransanci da kuma Mastas akan kasashe renonFaransa da kuma Arewacin Afurka, yayi karatunsa ne a jami’ar Bayero dake Kano. Sannan kwararre ne a harshe Larabcci da na Ingilishi”

“Wannan nadi da akai masa zai fara aiki nan take” A cewar sanarwar da mai magana da yawun Shugaban kasa ya fitar.

Idan za’a iya tunawa Shugaba Buhari ya sauke tsohon Shugaban hukumar Ayo Oke daga mukamin shugabancin a ranar 30 ga watan Oktoban 2017.

Sannan kuma yana daga cikin mutanan da kwamitin mataimakin Shugaban kasa ya bincikita kan batun badakala da aka zarge shi da yi.