
Shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil ya bukaci iyaye da su ba da muhimmanci ga sanya ido ga motsin ƴaƴansu domin dakile matsalar sace-sacen kananan yara a jihar.
Khalil ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake tsokaci game da sace kananan yara daga jihar Kano zuwa wasu sassan kasar nan.
Ya bayyana cewa kula da yara ba alhakin iyaye ne kadai ba, hakki ne na al’umma baki daya, d”on haka ya kamata mutane su hada hannu don tabbatar da tsaron ‘ya’yansu.”
“Yadda ake sace yaran mu a lokuta daban-daban ana kai su wasu sassan kasar nan, ana canza musu sunaye da addini, abin damuwa ne, don haka akwai bukatar al’umma su hada kai don tabbatar da tsaron yaran.” in ji Shehun Malamin.
Khalil ya ce yara su ne jagororin al’umma nan gaba, inda ya bukaci gwamnatoci a kowane mataki su kara zage damtse wajen kyautata tsarin kula da kananan yara a cikin al’umma.
Ya bukaci jama’a da su kara kaimi wajen gudanar da addu’o’in samun zaman lafiya a jihar Kano da Najeriya.