Home Labarai An sace yarinya ƴar shekara 5 a Kano

An sace yarinya ƴar shekara 5 a Kano

0
An sace yarinya ƴar shekara 5 a Kano

 

A yammacin  jiya Asabar, an jefa iyaye, ƴan’uwa da maƙwabta cikin wani hali na ɗaimaucewa da tashin hankali a unguwar Kawaji a Jihar Kano, bayan da a ka sace wata yarinya, mai suna Hanifa, ƴar shekara 5 kacal da haihuwa.
Rahotanni sun baiyana cewa an ɗauke Hanifa je lokacin da wasu su ka zo a babur mai ƙafa uku, inda su ka yi mata wayo su ka ɗauke ta.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a jiya Asabar da misalin ƙarfe 5 na yamma lokacin da Hanifa na dawowa da ga makarantar Islamiyya tare da sauran yara.
Da ya ke shaidawa jaridar DAILY NIGERIAN, ƙani ga mahaifin Hanifa, Suraj Zubair ya ce makarantar ba ta da nisa da gidan su yarinyar, inda ya ƙara da cewa sabo da rashin nisan, yaran unguwar sun saba zuwa makarantar da kan su.
“Mu dai labarin da mu ka samu daga yaran da lamarin ya faru a kan idon su, sun ce masu garkuwa da mutanen sun zo ne a babur mai ƙafa uku sai ku ce su zo su rage musu hanya. Bayan sun kawo so cikin unguwa, sai su ka ce Hanifa ta sake hawa su ɗana ta, da ga nan ne sai su ka tsere.
“A nan ne nake so amfani da wannan dama cewa duk wanda ya samu wani bayani a kan Hanifa da ya garzaya caji-ofis na kusa ya kai rahoto ko kuma ya kira wannan lambar wayar-  08032668195,”
Dama dai unguwar Kawaji ta yi ƙaurin suna wajen satar yara.
A unguwar ne ma a ka sace wani yaro mai suna Yusuf Nasiru a ranar 28 ga watan Disambar 2020.
Kano na fuskantar sace-sacen ƙanan yara inda har abin ya ta’azzara bayan da a ka gano wasu yara guda 9 da a ka sace a ka kai su jahohin inyamirai, a ka sai da su sannan a ka mai da su kiristoci.
Hakan ne ya sanya gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya kafa kwamitin bincike a kan yadda a ke keta haƙƙin yara ƙanana da a ka sace da kuma gano waɗanda ba a kai ga samo su ba.