Dan majalisar dattawa ta jihar Kogi Sanata Dino Melaye, ya bayyana yadda aka so yin garuwa da shi a yankin Gwagwalada dake babban birnin tarayya Abuja akan hanyarsa ta zuwa Lakwaja domin halartar kiran da kotu ta yi masa a ranar Alhamis.

Dino Melaye wanda dan majalisar dattawa ne, ya bayyanawa manema labarai a Abuja cewar, sai da ya fita a guje ya shige daji, sannan ya haye bishiya domin tsirar da rayuwarsa daga wadannan miyagun mutane.

Yace ranar Alhamis da sassafe ya bar Abuja domin zuwa Lakwaja don amsa kiran kotu, amma a hanyarsa ta tafiya ya lura da wata mota Toyota kirar Siyana tana biya da shi a baya, daga bisani kuma mutanan suka budewa motarsa wuta, inda suka yi yunkurin yin garkuwa da shi.

A ranar Talatar da ta gabata ne dan majalisar dattawa Dino Melaye ya koma jam’iyyar PDP mai adawa daga jam’iyyar APC, yana cikin jerin mutane 15 da Shugaban majalisar  dattawa Bukola Saraki ya bayyana komawarsu jam’iyyar PDP a zauren majalisar dattawa.