
Wata babbar kotun tarayya da ke zaman ta a Abuja, ta ɗage shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) zuwa watan Janairun 2024, yayin da zai ci gaba da zama a gidan yari har sai ya cika ƙa’idar belinsa ta kuɗi naira miliyan 300.
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) ce ta gurfanar da Emefiele bisa zargin sa da laifuka shida, ciki har da zargin badaƙala da kuɗi naira biliyan 1.6.
Sai dai tsohon gwamnan babban bankin ya musanta zargin.
Yanzu kotun ta ayyana 18 ga watan Janairun 2024 domin sake zama kan shari’ar.
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ne ya dakatar da Emefiele daga muƙaminsa a ranar 9 ga watan Yuli bayan “wani bincike da ake yi da kuma shirin sake fasalin ɓangaren kuɗi na ƙasar.
BBC Hausa