Tsohon mai baiwai tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara ta fuskar tsaro Sambo Dasuki

Kungiyar Iyalan Sultan Dasuki da aka fi sani da ‘Sultan Ibrahim Dasuki Progressive Asspciation’, SIDPA, ta yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya girmama umarnin kotu akan batun dan su Sambo Dasuki.

Kungiyar ta ce, a saki Sambo Dasuki, wanda tsohon mai baiwa tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara ta fuskar tsaro, daga inda ake tsare da shi ya dawo gida cikin iyalansa.

A wata sanarwa da kungiyar SIDPA ta rabawa manema labarai, wadda sakataren kungiyar Kabir T. Auwal ya sanyawa hannu, sanarwar ta bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, da ya girmama umarnin kotu da dokokin kasa, ya saki dan uwan su, sanarwar ta cigaba da cewa,iyalan sun yi shiru ne akan Sambo Dasuki, sabida suna zaton a gwamnatin demokaradiyya za’a bi ka’ida da kuma girmama umarnin kotu.

“Amma abin mamaki, yau kusan fiye da shekara biyu, Sambo Dasuki yana tsare bisa zalinci ba tare da wata kotu ta bayar da umarnin a tsare shi ba”

“Sana yiwa Sambo sharia’ah ne kawai a kafafen yada labarai, an tabbatar masa da laifi an ci zarafinsa duk a kafafen yada labarai, babu wata kotu da ta tabbatar masa da cewar shi mai laifi ne, sai dai kawai farfaganda da ake yadawa akansa, wannan Gwamnatin kuma tana gani ana yada abubuwan da ba gaskiya ba akansa amma suka kawar da kai” A cewar kungiyar SIDPA.

Kungiyar ta ce, ana tsare da shi tun kusan fiye da Shekaru biyu bisa zalinci da karya dokokin kasa, an sake shi, bayan kotu ta bayar da umarnin yin hakan, aka kuma kama shi bisa zalinci, an sake kama shi a Disambar 2015 bayan da ya cika dukkan sharudan bayar da belin da aka gindaya masa, amma Gwamnatin tarayya tayi burus da shi.

Kungiyar ta kuma kara da cewar, tun da aka tsare Sambo Dasuki, aka gabatar da shi gaban kotun tarayya, kotun kuma ta bayar da belinsa, haka nan, kotun ECOWAS, itama ba wai kawai cewa ta yi a sake shi ba, ta yi umarnin a biyashi diyyar Naira miliyan 15 na tsare shi da akai ba bisa ka’ida ba.

“Wakilan Gwamnatin tarayya, musamman hukumar tsaro ta farin kaya DSS, da kuma hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC dukkansu sun bijirewa umarnin kotuna akansa”

“Dukkanmu shaidu ne akan haka, wasu ma wanda suka aikata manyan laifuka kuma aka same su da laifi, duk an bayar da belinsu, bayan da ‘yan uwansu suka koka kan halin da suke ciki,amma shi kotu da kanta ta bayar da umarnin a sake shi amma anki bin umarnin kotu”

“A wannan al’amari na Sambo Dasuki, duk abinda ake cajinsa da shi ba wani laifi bane da za’a kasa bayar da belinsa ba, amma da gangan aka tauye masa hakkinsa, aka hana shi shaker iskar ‘yanci”.

“Kin amincewa ko bijirewa umarnin kotu da hukumomin tsaro suka yi akan batun Sambo Dasuki, wannan ba zai taba rasa nasaba da umarnin da suke samu daga Gwamnatin Buhari ba, wadda ta gaza matukar gazawa wajen yin adalci”

“Bangaren Shari’ah na Najeriya, yana bukatar sakar masa mara domin ya samu cin gashin kansa, ba tare da wani katsalandan daga bangaren zartarwa ba” A cewar kungiyar.

Haka kuma, kungiyar ta jaddada kira ga Gwamnatin tarayya da lallai ta bayar da Sambo Dasuki a matsayin beli kamar yadda tun farko kotuna suka bayar da umarni, sannan kuma, a cigaba da yi masa shari’ah a bayyana, ba yi masa shari’ah a cikin sirri ba, wadda kafafen yada labarai ke sharara karairayi akan ta.

“Tunda yanzu Najeriya ba kan tsarin mulkin kama-karya na soja take ba, to kuwa bai kamata a dinga karya kundin tsarin mulkin Najeriya ba, yana dacewa da bukatun wasu ba, dole a baiwa dan kasa ‘yancinsa kamar yadda kundin tsarin mulki ya bashi, indai ba kama-karya ake yi ba”

“A sabi da haka, muna kira da babbar murya ga Gwamnatin tarayya da ta girmamam tsarin Shari’ah, ta sakarwa Sambo Dasuki mara ya shaki iskar ‘yancinsa, indai bad a gangan Gwamnati tayi hakan ba, domin son ci masa mutunci da kuma cin zarafinsa”.