Mutum na farko da ya kamu da cutar Monkeypox daga Kano

A karon farko a jifhar Kano an samu ɓullar cutar nan da ake kira “Monkeypox”, a garin Tiga dake karamar hukumar Bebeji a yankin kudancin Kano, cutar da ke sanya jikin mutum yayi kuraje burɗun burɗun kamar kyanda.

Majiya mai tushe ta tabbatarwa da DAILY NIGERIAN cewar, mutumin da yake dauke da cutar da ya fito daga kauyen Nassarawan kuki, ya arce daga asibiti a ranar Laraba da daddare, bayan da bincike ya tabbatar da cewar yana dauke da cutar.

An kawwame mutumin a Asibitin a lokacin da bincike ya tabbatar da yana dauke da cutar, dan gudun kada ya yaɗa cutar zuwa ga sauran mutane, amma kuma mutumin ya tsare daga Asibitin a cikin dare.

Jami’an Asibitin sun ce, sun sanar da hukumomin Gwamnati kan samun  ɓullar wannan cuta, amma har ya zuwa yanzu babu wani bayani da zai kai ga gano inda mai dauke da wannan cuta ya sulale yayi ba.

Wakilinmu ya tuntubi Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dr. Kabiru Ibrahim Getso amma ya kasa samunsa ta wayar tangaraho har ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Sai dai a satin da ya gabata, Kwamashinan ya shaidawa manema labarai cewar, Gwamnati ta tanadi Asibiti na musamman domin duba duk wanda aka samu rahoton ya kamu da wannan cuta a jihar Kano.

A ranar 22 ga watan Satumbar nan Cibiyar kula da yaduwar cututtuka ta ƙasa NSDC, ta karbi rahoton samun ɓullar wannan cuta a asibitin koyarwa na yankin Neja Dalta dake Okolobiri a jihar Bayelsa.

Ya zuwa yanzu dai, kimanin mutum 43 aka tabbatar da sun kamu da wannan cuta a hukumance a jihohin Akwa Ibo da Cross Rivers da Ekiti da Legas da Enugu da Nassarawa da kuma jihar Rivers, sai kuma jihar Kano da aka samu ɓullar cutar a yanzu.

Ƙwararru sun tabbatar da cewar cutar na saurin bazuwa ne ta hanyar cuɗanya da masu ɗauke da wannan cuta, ko yin m’amala da dabbobin da suke ɗauke da wannan cuta kamar Biri da Gafiya da Ɓera da Burgu da sauran dangin waɗannan dabbobi.

Bayan haka kuma, mutane suna kaucewa kamuwa da wannan cutar ta hanyar kaucewa cin duk wani ɗanyen nama da bai dahu ba, sannan kuma a kaucewa shafar gumin wanda ake zargi ko aka tabbatar ya kamu da cutar, ko duk wani abu da ka iya fitowa daga jikin mutum da zai iya shafar wani.