Home Labarai Sanata Barau Jibrin na ƙoƙarin hana Shoprite barin Kano

Sanata Barau Jibrin na ƙoƙarin hana Shoprite barin Kano

0
Sanata Barau Jibrin na ƙoƙarin hana Shoprite barin Kano

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, ya samar da hanyoyi da zai tattauna da Shoprite, daya daga cikin fitattun manyan kantunan Najeriya, don su fasa rufe reshensu daya tilo a jihar Kano.

A tuna cewa kamfanin ya sanar a makon da ya gabata cewa ya yanke shawarar barin, Kano, cibiyar kasuwanci a watan Janairu, saboda ” kalubalen tattalin arziki ”.

Sai dai a wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai da bayanai, Ismail Mudashir ya fitar, ya ce Jibrin ya shirya ganawa da mahukuntan kamfanin a Abuja kan lamarin.

“Ofishin mataimakin shugaban majalisar dattawa ya tanadi hanyoyi don dakatar da ficewa daga Kano da Shoprite ke shirin yi.

“Mai girma mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I Jibrin, CON, zai gana da mahukuntan kamfanin a wannan makon inda za a tattauna batun da fatan za a warware.

“ batun kasuwanci ne tsantsa, amma za mu ga abin da za mu iya yi don shawo kansu su janye shawarar da suka yanke su ci gaba da zama a Kano.

“Kamar yadda muka sani, akwai dimbin damammakin kasuwanci a Kano, cibiyar kasuwanci ta Arewacin Najeriya. A lokacin da muke zawarcin masu zuba jari, ba za mu nade hannayenmu mu kyale su su tafi ba,” inji shi.