23.1 C
Abuja
Saturday, July 2, 2022

Ƴan sanda sun kashe ƴan bindiga 6 bayan daƙile wani hari a Katsina

Must read

 

Jami’an ƴan sanda a jihar Katsina, sunyi nasarar daƙile wani harin ƴan ta’adda a ƙauyukan Dabaibayawa da kuma Ɗantakiri dake ƙarƙashin ƙananan hukumomin Batagarawa da Dutsinma na jihar.

A yayin daƙile harin, jami’an ƴan sandan sun yi nasarar ƙwato shanun sata su 86 da tumaki tare da awaki 101.

Kakakin Rundunar Ƴan Sandan Jihar, SP Gambo Isah ya sanar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba.

Ya ce da yawa daga cikin ƴan ta’addan sun ranta a na kare bayan musayar wuta da jami’an tsaron ƴan sandan a inda suka jikkata sakamakon harbin bindiga.

Ya zuwa yanzu dai, ana ci gaba da gudanar da ran gadi a dazukan dake maƙwabtaka da inda al’amarin ya faru domin chafke ko kuma gano gawarwakin ƴan ta’addan da suka tsere da raunuka daban-daban tare da makaman da suke tu’ammali da su.

labaran duniya na yau

More articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Latest article