Home Labarai ‘Sankarar mahaifa na kashe mata 28 kullum a Nijeriya’

‘Sankarar mahaifa na kashe mata 28 kullum a Nijeriya’

0
‘Sankarar mahaifa na kashe mata 28 kullum a Nijeriya’

Wacce ta kafa gidauniyar Breast Without Spot, Farfesa Ifeoma Okoye, ta ce cutar kansar mahaifa na kashe mata tsakanin 23 zuwa 28 a kullum a Najeriya.

Misis Okoye ta bayyana hakan ne a yayin gangamin wayar dakai na gidauniyar Goodway tare da hadin gwiwar gidauniyar Breast Without Spot, wanda aka gudanar a ranar Litinin a unguwar Ikotun da ke Legas.

Ta ba da shawarar yin gwaje-gwaje na yau da kullum don hana yawan mace-mace daga cutar ta kansa.

Ta ce, “An lura cewa ƙwararrun ma’aikatan kiwon lafiya sukan fuskanci ƙalubale yayin da yawancin marasa lafiya suka nemi kulawar likita a matakan ci gaba na cutar.

“Wannan na iya sanya nauyi mai yawa akan samar da kayan aikin kiwon lafiya, tsadar kiwon lafiya kuma yana iya daƙile fatan ci gaba da rayuwa ga marasa lafiya.

“Kansar mahaifa na kashe mata 23 zuwa 28 a kullum a Najeriya. Don haka, ta hanyar gudanar da gwaje-gwaje akai-akai a ɓangaren mama da al’aura, za a iya rage barazanar kamuwa da cutar daji kamar sankarar mama da sankarar mahaifa, da sauran nau’o’in ciwon daji da ka iya shafar jiki.”

A cewarta, mata na jin kunyar ƙyama da fargabar da mazajensu ke yi musu, don haka sukan boye yanayin su koda ga masu neman mafita.