'Yar wasan barkwanci daga kudancin Najeriya, Emmanuella

Daga Anas Saminu Ja’en

Duk da ba a taru an zama daya ba a Social Media din akwai mutane gurbatattu amman kuma akwai masu kirki masu ilimi wadanda suka san ya kamata, A yankin Arewa an dauki duk wani wanda zai dauki waya ya yi rubutu a matsayin dan zaman banza wanda bai san ciwon kansa ba. Abun da mutane suka manta shi ne kowane dan adam yana da baiwar da Allah ya yi masa ta kowane fanni na rayuwa.

Misali: Akwai da yawa matasa a arewa masu amfani da wayoyin hannu na zamani suke rubuce-rubuce na nuna kauna da kare martabar wani ko wata musamman a bangaran siyasa, kaga matashi ya yi bakin jinin duniya a zageshi a ciwa iyayen sa mutunci amman saboda takaici wanda yake karewa babu ruwansa da shi idan dan siyasa ne lokacin da ya samu nasara lokacin zai raba hanya da shi, babu ruwansa da tallafawa rayuwar sa.

Matasa suna amfani ne da basira da kudin su ya kamata a ce ana agazawa basirar ta su domin cimma ga ci ta fuskar karo karatu amman babu ruwan su, kuma abun takaicin shi ne zaka nuna rashin ko’inkula da wanda yake kaunarka babu dare babu rana, Ta ya wanda yake nuna maka waccar kaunar zai ji idan har ya fuskanci kai da yake yi domin kai kuma baka kaunar ci gaban rayuwar sa idan har ya waiwayeka ya dawo mai sukar ka.

Wannan abubuwan sune suke sakawa matasan arewa masu yin Social Media jin ciwo suna yin wahala dan mutun amman kuma shi ba ruwan sa da su ga dama ta samu a siyasan ce sai a haye su bayan kowa ba ya san ita fa siyasar nan ba dan Allah ake yin ta ba harka ce kurum ta biyan bukatar kai. ita kuwa zuciya tana bukatar mai kyautata mata a koda yaushe kuma ko ya ya ne, amman babu takaici kana nunawa mutun kauna amman shi da ‘yan uwan sa suna kallon ka dan iska suna ganin ai wayon su ne yake kai su matsayin da har kai kake son su kake kare musu mutuncin su.

Yanzu ku dubi shugaban majalissar dattawa Bukola Saraki inda yake neman kyautawa wadda yake kauna. kuma ya ajiye misali mai kyau ga ‘yan siyasa da sauran mutane, Ya gayyaci Yarinya Emmanuella mai yin wasan barkwanci zuwa gaban su a majalissa domin su tallafa mata da kudade wanda zata inganta harkokin ta na barkwanci, ka ji masu son ci gaban al’umma ga dukkan alamu Bukola yana jin dadin kallon wasan barkwanci kuma yake ganin tana bukatar taimako. Tabbas Emmanuella da iyayen ta, ‘yan uwa ta da kwayenta ba za su manta da Bukola Saraki ba domin ya kyauta sosai.

A arewa muna da matasa maza da mata masu basira ta huce tunani amman saboda da rashin matallafi sai mutun ya kare a cikin wahala, kuma babu mai kwatanta haka kullum shi yasa yara suke ciwa ‘yan siyasa zarafi a Social Media saboda ba su taimake su ba, amman kuma lokacin da suke neman kujerin da suke kai sun nemi taimakon matasan.