Ooni Na Ife, Adeyeye Ogunwusi

Ooni Na Ife, Adeyeye Ogunwusi ya baiwa yara 270 tallafin karatun Sakandire a yankin kasashen Yarabawa a shekara biyu da suka gabata.

Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin Adeyanju Olaoluwa, mai lura da sashin bayar da tallafin karatun na yankin kudu maso yamma, ya bayyana hakan ne a lokacin da daliban da suka ci gajiyar wannan tallafi suka kaiwa Sarkin ziyarar godiya da nuna jindadi”

Mista Olaoluwa ya bayyana cewa daga cikin irin abubuwan da Ooni na Ife ya cimma a tsawon shekaru biyu na mulkinsa har da wannan tallafi da yake baiwa bangaren karatun Sakandire domin tallafawa masu karamin karfi.

A cewarsa, Sarkin ne ya nemi ya bayar da sunayen daliban da ba zasu iya biyan kudin makaranta domin ya tallafa musu da biyan kudin makaranta. A sabida haka muka zakulo yara daga makarantu 37 da suke da matsalar biyan kudin makaranta.

Ya kara da cewar, akwai dalibai 68 da aka biyawa kudin rubuta jarabawar WAEC a cikin makarantu 23 dake fadin kasar Yarabawa ta kudu maso yamma.

Da yake mayar da jawabi a lokacin da daliban suka ziyarce shi, Ooni na Ife ya yiwa Allah godiya da ya bashi ikon tallafa musu da kudin makaranta har suka cimma burinsu na samun ilimi.

Sarkin ya kuma ja hankalin daliban da cewar kada su taba yanke tsammani a rayuwa, su kyautata zato ga Allah kuma su dage zasu ci nasara.

Yemi Opawoye-Adeagbo mataimakin Shugaban makarantar Ilobu ya yi godiya ta musamman ga Sarkin a madadin daliban ya kuma yi masa adduah da fatan alheri.