Home Labarai Sarkin Musulmi da Ƙungiyar CAN sun buƙaci a dakatar da zanga-zanga nan take

Sarkin Musulmi da Ƙungiyar CAN sun buƙaci a dakatar da zanga-zanga nan take

0
Sarkin Musulmi da Ƙungiyar CAN sun buƙaci a dakatar da zanga-zanga nan take

Majalisar mabiya addinai ta Najeriya NIEREC karkashin jagorancin mai Alfarma Sarkin Musulmai , Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar da shugaban kungiyar CAN ta kasa, Archbishop Daniel Okoh sun yi kira ga ‘yan Najeriya da su gaggauta dakatar da zanga zangar da suke yi a fadin Najeriya.

Sun yi kiran ne a wata sanarwa da suka fitar a yau Juma’a mai dauke da sa hannun Sakataren majalisar, Farfesa Cornelius Afebu Omonokhua.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa an hallaka mutane da dama a yayin zanga zangar da illata mutane da dama.

“NIREC ta lura da abubuwan da suka faru a wannan yanayi. Zanga zangar wacce ta fara cikin lumana a ranar 1 ga watan Agusta ta juye ta koma rikici”.

“A wanni kadan bayan hakan, an fara samun asarar rayuka da dukiyoyi”, inji sanarwar.

Majalisar ta ce ta lura da irin yanayin da ake ciki na matsin tattalin arziki sai dai ta ce tashin hankali ba zai kawo masalaha ba.

Haka kuma ta yi kira ga hukumomin tsaro da su tafiyar da lamarin cikin gogewa.