Home Labarai Sarkin Zazzau ya naɗa ɗan sa a matsayin Walin Zazzau

Sarkin Zazzau ya naɗa ɗan sa a matsayin Walin Zazzau

0
Sarkin Zazzau ya naɗa ɗan sa a matsayin Walin Zazzau

Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, CFR, ya amince da nadin ɗan sa na fari, Abdullahi Ahmed Bamalli a matsayin sabon Walin Zazzau.

Hakan ya biyo bayan rasuwar tsohon Walin Zazzau kuma Hakimin Ikara, Injiniya Aminu Umar, wanda ya rasu bayan gajeriyar jinya a ranar Lahadi.

Daily Trust ta gano cewa sarautar Wali a Masarautar Zazzau ita ce ta uku a cikin manyan hakimai da sarakunan masarautar ke rike da su bayan sarautar Madaki da Magajin Gari.

A wata sanarwa da Abdullahi Aliyu Kwarbai, jami’in yada labarai da bayanai na masarautar ya fitar, ta ce kakan Abdullahi Bamalli, Marigayi Walin Zazzau, Halliru ne ya fara rike sarautar.

Sanarwar ta kuma ƙara da cewa Sarkin ya kuma amince da nadin Injiniya Sani Galadima Umar, kanin marigayi Walin Zazzau, Injiniya Aminu Umar a matsayin sabon Yariman Zazzau.

A tuna cewa tsohon Yariman Zazzau, Alhaji Munir Jafaru, shi ne tsohon Yariman Zazzau wanda tun daga lokacin ne sarki ya ɗaga likkafar sa zuwa matsayin ‘Madaki Zazzau