Home Labarai Saudiyya ta rage yawan Alhazan Najeriya a bana

Saudiyya ta rage yawan Alhazan Najeriya a bana

0
Saudiyya ta rage yawan Alhazan Najeriya a bana

A bana maniyata sama da dubu hamsin ne za su yi aikin Hajjin bana, sabanin dubu chasa’in da biyar, kuma tuni har an riga an kwashe alhazai dubu goma sha daya da dari hudu, wadanda a bana suna sauka a birnin Madina ne kai tsaye.

Shugaban hukumar Alhazai na ‘kasa, Barista Abdullahi Muktahar ya ce rage yawan Alhazan da aka yi ya biyo bayan wani matakin aiki ne da hukumomin Saudiyya suka gindaya, domin ta san yawan bakin da zasu je kasar don yi musu tanadi.

Sai dai kuma a Najeriya, bayanai sun nuna cewa sai makonnin biyun karshe da za a rufe filin jirgin sama ne wasu mutane ke biyan kudinsu na zuwa Makka.

Barista Abdullahi dai yayi kira ga masu kula da ayyukan hajji da masu ruwa da tsaki, da cewa ka da su bari masu suka su karkatar da hankalinsu, wajen bin ka’idoji da dokokin da aka gindaya, musamman don gudanar da ayyuka cikin nasara.

VOAHAUSA.COM