Haƙiƙa zaɓen kujerar gwamnan jihar Kano, zaɓe ne tsakanin guguwar wasu mutane masu neman a koma baya, ƴan a fasa kowa ya rasa. Da kuma masu angiza dukiyar al’ummar jihar cikin aljihunansu, marasa tausayin talakawa. Dukkanin waɗannan za su buga ne da rundunar masu tsayuwa akan manufa ta ceto talakan jihar Kano daga uƙuba, fatara zalunci da babakeren mahukunta, mahandama ƴan bani-na-iya kuma masu almundahana da dukiyar al’umma ba tare da haƙƙi ba.

Ƙungiyar farko masu neman a ba su damar mulkin jihar, ka iya kiransu da wata irin tawaga masu kama da ƙungiyar asiri, wacce in ba ka saka wata alama mu’ayyana ba, ba su ɗaukarka a matsayin abokin tafiya. Mutane ne masu tsabagen biyayya ga wata aƙida, wacce ka iya cewa aƙida ce ta tunanin wani mutum ɗaya tilo wanda saɓa masa ya kan zama wani babban zunubi a ɗarikar.

Ƙarkashin mulkin wannan tawaga dai an sayar da manya da ƙananan gidaje mallakar jihar aka handame kuɗaɗen ba a kuma gina wasu a madadinsu ba.

Wannan ƙungiyar su ne dai suka afka jihar cikin ƙangin talauci wajen maƙure maƙoshin ƙananan hukumomi 44 na jihar a tsawon shekaru takwas da suka shafe a karagar mulki. Ta hanyar ƙin baiwa ƙananan hukumomin kuɗaɗensu.

Su ne dai suka barwa jihar bashin sama da naira Bilyan 300 bayan sun bar mulki. Ƙungiyar ta samu damar handame kuɗaɗen ƴan fansho na jihar, su ne dai suka gaza biyan bashin sama da Naira Bilyan 6 na kuɗaɗen ƙaro karatu na daliban jihar kano.
Haka nan sun yi ƙaurin suna wajen babakere ga dukiyar al’umma.

Ƙarkashin mulkinsu an tabbatar sun shahara wajen aiwatar da tituna da ayyuka marasa inganci a duk faɗin jihar ta Kano. Ban da uwa uba karɓe 10% na tituna na kilomita 5 a ƙananan hukumoni 44 na jihar ba tare da nuna ko ƙwaya ɗaya da suka kammala ba.

Ɓangare na biyu wata tawaga ce ta mayaudara, maha’inta masu handama da aka kama dumu-dumu
da laifin karɓar na-goro wajen aiwatar da ayyukan raya ƙasa a jihar. Mutane ne masu uwa a gindin murhu dalilin da ba za a iya hukunta su a bisa laifin da suka tafka ba.

Tawaga ce da suka fake da dattaku da gaskiyar babban jagoran ƙasar domin yaudarar talakawa na cewa irin aƙidarsu ɗaya ta gaskiya da wancan shugaba. Su ma dai kamar waccen ƙungiya ta farko babu tausayin talakan da ya zaɓe su kusan shekaru 4 kenan da suke kan mulki. Talakan jihar bai gani a ƙasa ba, domin sun gaza wajen inganta kasuwanci wanda shi ne babbar sana’ar mutanen jihar. Sun gaza wajen inganta harkar noma inda har wasu ƙananan jihohi suka shiga gaban jihar Kano a harkar noma.

Guguwar mutane ce wacce ta tsunduma Kano a matsalar ƙarancin ruwa a sassa mafi yawa na jihar Kano. Saboda sakaci da rashin tarbiyantar da al’umma ya sa jihar ta dauki lambar; Jiha mafi yawan matasa mashaya a ƙasar. Wannan tawaga ta yi sanadiyyar dawowar siyasar ƴan daba inda ake kashe-kashe tsakanin ɓangarorin ƴan daba da ma mutanen da basu ji ba basu gani ba.

Runduna ta uku da suke neman ɗarewa karagar mulkin Kano su ne waɗanda aka zalunta, aka ƙwacewa matsayin da ya kamata a basu a baya. Tawaga ce ta adalci masu sanin ya kamata, masu manufa da basu yarda an mallake tunaninsu da kaifin basirarsu don biyayya ido rufe ga wani madugun wata ɗarika ba.

Rundunar nasara, mutane ne masu manufa da tsari da burin ɗora jihar Kano a mizanin jihar da za ta yiwa sauran jihohi fintinkau wajen tattalin arziƙi, noma kiwo da bunƙasa ƙananan sana’oi.

Kano za ta dawo da martabarta a idon duniya, na zaman ta jiha mafi bunƙasar kasuwanci da zaman lafiya, tarbiyya, gami da al’amuran addinin musulunci.

Saboda haka wanann tawaga ta ceton talakawan jihar ƙarkashin aƙida irin ta malam Aminu Kano ta saka Halifa na ƙwarai wanda zai ɗora jihar a bisa tsarin da ya kamaceta. Ɗan takarar gwamna a ƙarkashin jam’iyya mai Makulli wato P.R.P., Mal Salihi Sagiru TAKAI.

Malam Salihu Muhammad Sagir Takai dan siyasa ne, kuma manomi. Malam mutumin kirki ne ɗan ƙwarai, mai amana, dattijo da ko kaɗan ba shi da girman kai. Gwarzon shugaba ne managarci wanda ba shi da kasala, yana tafiyar da al’amuransa lillahi, babu nuƙu-nuƙu ba almundahana, mai haƙuri da juriya, uwa uba kuma mai riƙo da addini ne.

Lallai Bahaushe ya yi gaskiya da ya ce ; Sayen Nagari mai da kudi gida.

Ado Abdullahi