
Sanata George Akume, Sakataren Gwamnatin Tarayya, SGF, ya yi gargadi kan masu amfani da ofishin sa wajen cuwa-cuwar ɗaukar aiki ga jama’a.
Akume ya yi wannan gargadin ne a wata sanarwa da Segun Imohiosen, shugaban sashin yada labarai na ofishin SGF, ya fitar a jiya Lahadi a Abuja.
Ya ce wannan gargadin ya biyo bayan ɗaukar aiki na bogi da wasu marasa gaskiya ke fitowa da shi daga ofishin SGF na damfarar mutanen da ba su ji ba gani.
Akume ya barranta ofishin sa da bayanan ƙarya da ke yawo a kafafen sada zumunta, imel, sakon kar-ta-kwana, da sauran kafafen yada labarai da ke yaudarar jama’a da su mika takardun su da kuma kudi, ga wani ofishin daukar aiki da ofishinsa bai san da shi ba.
“Mai laifin yana amfani da sunan tsohon Daraktan Yada Labarai, Willie Bassey, da wadannan abokan hulda na yaudara; Aliyu Isah; +234 9168487156, +234 8035557865 da imel; draliyu95@gmail.com, da dai sauran su domin damfarar ’yan Najeriya da basu ji ba basu gani ba
“A bisa wannan sanarwar an ba jama’a shawarar da su yi taka-tsan-tsan da masu aikata wannan laifi da ‘yan kungiyarsu; da kuma yin watsi da irin waɗannan bayanan da ke fitowa.
“Duk wani bincike na hukuma da bayani ya kamata ya bi hanyoyin sadarwa na hukuma na OSGF ta www.osgf.gov.ng da info@osgf.gov.ng,” in ji shi.