
Ɗan takarar gwamnan Jihar Kano a jam’iyar APC, kuma ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Kano Municipal, Sha’aban Sharada, ya kai ziyarar bazata wajen da za a gudanar da zaɓen fidda-gwani na gwamna a jihar.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa za a gudanar da zaɓen ne tsakanin Mataimakin Gwamnan Kano, Nasiru Yusuf Gawuna, kuma ɗan takarar gwamna a APC a jihar da kuma Sharada.
Zaɓen dai zai gudana ne a filin wasa na indoor Stadium da ke Kofar Mata a birnin Kano a yau Alhamis.
Sai dai kuma wasu hotuna da su ka fara yawo a kafafen sadarwa sun nuna Sharada, tare da muƙarrabansa, ya shiga wajen da za a gudanar da zaɓen, domin duba irin shirin da a ka yi a zaɓen.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne dai ya tsayar da Gawuna, da tsohon Kwamishinan Ƙananan Hukumomi, Murtala Sule Garo a matsayin waɗanda za su yinwa APC takara a APC.
Sannan shima Sharada, wanda ya ke cikin ɓangaren G-7 a APC, ya tsaya takarar, inda a yau ne za a raba raini tsakaninsu domin fitar da wanda zai jagoranci jam’iyar a zaɓen gwamna na 2023 a jihar.