Daga Danladi Haruna
Lokacin da Shehu Jaha yana alkalanci a birnin Aku Shahar, sai ga wasu mutane sun zo gabansa suna rikici kamar sa naushi juna. Da suka gurfana gabansa ya daka musu tsawa ya ce, “me yake tafe da ku? Kun san nan kotu ce, ba a mana wargi anan!”
Daya daga ciki ya mike ya ce, “Allah ya gafarta Malam wannan gurmina ne aka dauke min yau kwana uku ina nemansa na ganshi a hannun wannan mutumin yana kadawa ana ba shi kudi. Na zo gabanka ne domin a karbar min kayana.” Alkali Shehu Jaha ya dubi wanda ake kara ya ce, “ka ji abin da ake kararka da shi. Haka ne? Dauke masa ka yi?” Mutumin ya ce, “gafarta Malam na tabbata dai ba nawa ba ne, amma shi ma ba nasa ba ne, tunda tsinta na yi a wuri kaza.”
Alkali ya ce da mai kara, “kana da shaidu? Kuma da wata alama a jikin gurmin naka?” Mai kara ya ce, “eh daga wuyan gurmin akwai inda aka yi ‘yar k’ofa inda ake dura mai saboda ya yi laushi, sannan daga kasansa akwai wata alamar maciji da na zana. Har ila yau akwai shaidu mutum biyu da suka san wannan gurmin nawa ne tun da jimawa.”
Alkali ya sa aka duba gurmi aka ga alamun da ya fada haka suke, sannan aka shigo da shaidu suka shaida tabbas gurmi mallakinsa ne. Ba tare da bata lokaci ba alkali Shehu Jaha ya sa aka kwace gurmi daga hannun daya aka mikawa mai shi. Sai kuwa wanda aka kwace gurmin daga hannunsa ya yi farat ya ce, “Allah ya gafarta Malam ban yarda da shaidun wadannan mutanen ba. Domin na farko yaron mai dafa giya ne, na biyu kuma dan wankin gidan karuwai ne.”
Shehu Jaha ya ce, “Shaidu sun cika yadda ake bukata, domin kayan banza mutanen banza ne ke shaida akansu. Da alk’urani ne ko wani abin kirki ba za mu karbi shaidunsu ba.”