Fitaccen Malamin addinin Musulinci a Najeriya Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bayyana goyon bayansa ga Femi Gbajabiamila a matsayin kakakin majalisar wakilai ta 9.

Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana goyon bayansa ga Femi ne a Makkah yayin da zababben dan majalisa mai wakiltar Darazo da Ganjuwa ya jagoranci Femi zuwa masaukin Malamin dake Makkah.