
Wani ibtila’i ne ya afku a jiya Lahadi, yayin da wani mutum da har yanzu ba a kai ga gane ko wanene ba ya rasa ransa a wata gobara da ta tashi da tsakar dare a yankin Bariga da ke jihar Legas.
PUNCH Metro ta tattaro cewa gobarar da ta faru da misalin karfe 3 na safe, ta kone ɗakuna 10 a cikin wani gida mai ɗakuna 25 da shaguna 18.
An samu labarin cewa wata gobara ta sake afkuwa a wani gida mai dakuna takwas da shaguna hudu a yankin Somolu na jihar.
Daraktar hukumar kashe gobara ta jihar Legas, Margaret Adeseye, ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ta fitar a jiya Lahadi.
Ta ce, “Hukumar kashe gobara ta jihar Legas cikin dare ta yi nasarar kashe gobara guda biyu a yankin Bariga da Somolu na jihar.
“An sanar da na farko cikin gaggawar ne da misalin karfe 12:31 na safiyar Lahadi, zuwa 19, titin Apata, Somolu, yayin da aka sanar da daya daga karfe 3.19 na safe zuwa 48, titin Jagunmolu, Bariga, a daidai lokacin da aka kammala aikin kashe gobara.