
Gamayyar Kungiyoyin Matasan Arewa masu rajin Zaman lafiya da Kwanciyar Hankali sun sha alwashin ba za su shiga zanga-zangar da ake shirin yi a fadin kasar ba.
A wata sanarwa da ya fitar a yau Alhamis, Kodinetan kungiyar, Yazeed Tanko, ya ce zanga-zangar ba ta da wani cikakkiyar manufa da jagoranci.
A cewarsa, zanga-zangar za ta kara tabarbarewar matsalolin tsaro a kasar.
“Ina kira ga matasan Najeriya musamman ‘yan uwanmu na Arewa da kada su shiga wannan zanga-zangar. Kamar yadda kuke gani shugaban ƙasa ya fara mayar da martani kan batutuwan. Kwanan nan ne aka aika da manyan motocin shinkafa zuwa jihohi, kuma an amince da sabon mafi karancin albashi ga ma’aikatan gwamnati.
“Kuma yayi alƙawarin zai kara yi. Don haka mu kara bashi lokaci”.
Mista Tanko ya kara da cewa, “da farko mun yarda mu shiga zanga-zangar, amma daga baya mu ka fahimci cewa wasu batagari na shirin fakewa su aikata ba daidai ba.
Shi ya sa a lokacin da shugabanninmu da malaman Musulunci suka yi gargadin suka ja hankalinmu zuwa ga gaskiya, sai muka fasa shiga
“Mu mutane ne masu mutuntawa ds da’a, amma kuma wasu sun yarda da a yi amfani da mu wajen ruguza kasar nan”.