Daga Rilwanu Adamu Diso

Da za’a jeranta buqatun talakan Kano ginin gada ba zai zo a na d’ari ba a halin da ake ciki a yanzu. Yanzu fa abin yafi k’arfin talauci ko jahilci a yadda ake kallon su, magana ake ta d’imauta da rashin sanin inda aka sa gaba a rayuwa sakamakon zare hannu da gwamnati tayi daga ainihin abin da talaka yake buqata don ya rayu ta mai da hankali ga buqatun kankin kanta kad’ai. Wannan tasa rayuwa ta koma makamanciyar rayuwar da akai lokacin fatara ( lokacin da ba saqon annabta ) kowa neman hanyar tsira yake ba ruwan sa da halacci ko haramci saboda dole yana buqatar yaci ya sha ( wamaa ja’alnaakum jasadan laa ya’akulunad’d’a’ama) kuma dole ya nemi magani in bai da lafiya.

Ban san iyakar shagunan da aka b’arke da gidajen da aka haura akai fashi a kewayen mu a y’an kwanakinnan ba. Harda bindiga aka shigo loko aka b’arke shago aka kwashe kayan ciki gabad’aya yau bai wuce sati ba. Abin ya wuce yadda ake zato. Ba abin da zai magance wannan sama da ingantawa al’umma tattalin arzikin ta da kuma tarbiyantar da ita. Sannan duk yadda kakai da wadata d’an’adam inbai da tarbiya bazai ji ya wadatu ba kuma duk hanyar da zai bi don wadatar da kan sa zai bi ta. Kuma baka da yadda zaka tarbiyantar da al’umma sama da amfani da abin da tai imani da shi na addini.

Mu tamu al’ummar dole da musulinci zaka tarbiyantar da ita sai ya zamana kok’ak’a mutun ya samu na kai wa bakin salati sai ya godewa Allah. Don haka sai an gwama inganta tattalin arziki tare da tarbiyantar wa. Kaso d’aya bisa goman kud’ad’en da aka kashe wajan gina gadajen nan na Kano zai isa a gyara dama-daman Kano sama da goma wanda hakan zai samar wa da miliyoyin mutane aiki kuma abinci zai wadatu a sauqaqe. Duk yankin da kai musu wannan ka sallame su, y’ay’an su baza su watsu barace barace ba ballantana su b’uge da ayyukan ta’addanci kamar yadda yake faruwa a yanzu. Shi yasa zai wuya kaga almajiri daga yankin karamar hukumar Kura.

Abu na biyu, sai ka qarfafi hukumomin da suke da alhakin tarbiyantar da al’umma irin su Hizba da hukumar Shari’a. Inkai wannan had’i da wasu dabarun kamar yadda nauyin tunanin hakan yake kan mai mulki kaiwa al’umma abin da ya dace da dukiyar ta kuma ka nuna sanin makama a mulki. Amman ginin gada ba wata hikima ciki kuma kai kad’ai zai anfanar ta hanyar kashe mu raba da y’an kwangila. Kud’in da gwamnatin tarayya take antayo wa kowa na da haqqi a ciki, don haka lallai lallai gwamnatin Kano ta canja shawara.