Shugaba Muhammadu Buhari yayin da yake gabatar da daftarin kasafin kudin 2018

Kamar yadda ya alkawarta, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau talata ya gabatar da daftarin kasafin kuɗi na kimanin Naira tiriliyan 8.613 a gaban haɗakar ‘yan majalisun dattawa da na wakilai.

Shugaban majalisar dattawa Dr. Bukola Saraki da kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara ne suka tarbe shi a harabar zauren majalisar wakilai ta kasa a Abuja. Shugaban kasar ya gabatarwa da majalisun manyan jakunkuna guda biyu da suke kunshe da daftarin kasafin kudin.

A yayin da yake gabatar da jawabinsa, Shugaba Buhari yace, kasafin kuɗin shekarar 2018, zai sanya farin ciki a zukatan ‘yan Najeriya. Shi dai kasafin anyi shi ne,akan za’a sayar da gangar ɗanyen mai akan dalar Amurka 45 kimanin naira 305. Yayin da za’a dinga hako gangar danyen mai miliyan 2.3 a kowacce rana

Haka kuma, manyan ma’aikatun da aka ware musu kudade masu yawa da suka hada da na manyan ayyuka da albashi sune, ma’aikatar cikin gida an ware mata naira biliyan 510.87, yayin da ma’aikatar ilimi aka ware mata naira biliyan 435.01, sai kuma ma’aikatar tsaro naira biliyan 422.43, sannan kuma,ma’aikatar lafiya naira biliyan 269.34.

Sauran ma’aikatun sun hada da ma’aikatar ayyuka da makamashi da gidaje naira biliyan 555.88, ma’aikatar sufuri naira biliyan 263.10, yayin da, ayyukan na musamman ta samu naira biliyan 150.00. Albarkatun ruwa naira biliyan 95.11.

A wannan kasafin kudi an warewa aikin katafariyar gadar nan da ake kira “Second Niger Bridge” naira biliyan 10.00. yayinda aikin wutar lantarki na Mambila aka ware masa naira biliyan 9.8. Sannan akwai aikin gina manyan hanyoyi da aka ware masa naira biliyan 300.

Bayan haka kuma, shugaban yace gwamnatinsa zata cigaba da aiwatar da shirin nan na rabawa mutane kudi kyauta na naira 5000 ko wanne wata, da kuma shirin ta na ciyar da daliban firamare abinci kyauta.

Shugaban ya kara da cewar, fiye da yara miliyan 4.5 ‘yan aji daya zuwa hudu ake ciyarwa a kowacce rana a makarantun gwamnati na firamare. Sannan gwamnatinsa karkashin shirin nan na daukar matasa aikin koyarwa na N-power, an dauki kusan mutum 200,000 aiki ana biyansu albashi duk wata.

Haka kuma, fiye da mutane 250,000 suka amfana da shirin koyawa matasa sana’o’i, wanda ya lashe zunzurutun kudi naira biliyan  12.5, haka kuma, fiye da mutum 110,000 ne suka amfana da shirin tallafin naira 5000 a duk fadin Najeriya.

Shugaban ya gama jawabinsa da cikakken fatan cewar, ‘yan majalisu zassu tattauna domin bayar da damar sanyawa daftarin kasafin kudin hannu, don ya fara aiki ba tare da bata lokaci ba, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar.

Sai dai, da shugaban majalisar dattawa ya tambayi shugaban kasa kan yadda aka aiwatar da kasafin kudin shekarar 2017, shugaba Buhari ya baiwa ‘yan Najeriya hakuri, yana mai cewar, shekarar 2017 ta zo cike da kalubale, musamman a manyan kasashen duniya wanda ya shafi Najeriya kai tsaye.

Sai dai shugaban ya tabbatar da ‘yan Najeriya cewar, a wannan shekarar mai kamawa ta 2018 al’umma zasu yi baja baja, domin kuwa kasafin kudin an tsara shi domin amfanin ‘yan Najeriya kai tsaye, kuma zasu yi murna da shi a cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari.