Shugaba Buhari tare da wasu daga cikin Gwamnonin Najeriya

A yau Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gana da tawagar gwamnonin Najeriya a fadar Gwamnati dake Aso Rock Abuja.

Shugaban kungiyar Gwamnonin Najeriya, kuma Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari Abubakar shi ne zai jagoranci gwamnonin zuwa fadar Shugaban kasa da ranar nan.

Har ya zuwa yanzu dai ba a san ko akan meye zasu tattauna ba. Zuwa jimawa zamu kawo muku cikakken rahoto.