Categories
Siyasa

Shugaba Muhammadu Buhari na fama da zurarewar magoya baya – Mustapha Panandas

Shugaban kungiyar ‘yan a-mutun Buhari na kasa, Alhaji Mustapha Panandas ya bayyana cewar, magoya bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari na zurarewa a kullum, sabida dalilin da ya bayyan, na cewar ‘yan siyasar Abuja sun hana shugaban sakat.

Panandas ya bayyana hakan ne a Abuja, a wata sanarwa da ya rabawa ‘yan jaridu. “shugaban kasa Muhammadu Buhari, mutum ne na kowa da, ‘yan Najeriya ke matukar kauna, bisa kyakkyawan zaton da suke yi masa”

“Mutum mai tsananin kishin ganin cigaban kasarnan, tare da fatan cirewa talakawa suhe daga wuta, amma wasu tsiraru sun sanya shi a aljihunsu, sai yadda suka ga dama suka yi da shi. ABinda kawai suke so shi ake aiwatarwa a daga Abuja”

“Tilas ne shugaba Buhari ya kakkabe, wadannan miyagun mutane da suka kanainayeshi, indai yana son kansa da alheri kafin zaben da yake tafe, domin akwai masoya da magoya baya na hakika da suke kasa, suna yiwa shugaba fatan alheri da fatan samun nasara” A cewar Alhaji Mustapha Panandas

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *