Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da kasafin kudin shekarar 2019 a gaban hadakar zauren majalisun dokoki da na dattawa.

‘Yan majalisun dokoki na tarayya sun dinga ihu tare da fadin Sai Buhari a lokacin da Shugaban ya iso zauren majalisar wakilai ta kasa domin gabatar da kasafin kudin.