
Domin kawo sauki da ake buƙata ga rayuwar ƴan Najeriya da kuma tabbatar da ingancin shirye-shiryen jin kai da ci gaban al’umma, Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin wasu kwararrun ƴan Najeriya guda bakwai da za su jagoranci hukumomi da tsare-tsare a karkashin ma’aikatar jin kai da magance ibtila’i da ci gaban al’umma ta tarayya.
Waɗanda shugaban ya naɗa sun haɗa da:
(1) Dr. Badamasi Lawal — Shugaban Shirin Rabon Tallafi ga Al’umma (NSIPA)
(2) Madam Funmilola Olotu — Manajar Shirye-Shirye, Ofishin Gudanar da shirin Safety-Net na Kasa
(3) Malama Aishat Aubankudi — Manajar Shirye-Shirye, Tallafin Ƙungiyoyin Marasa Galihu
(4) Gimbiya Aderemi Adebowale — Manajar Shirye-Shirye, Ciyar da Ɗalibai a Makarantun Cikin Gida.
(5) Malam Abdullahi Alhassan Imam — Manajan Shirye-Shirye na Ofishin Shirin Tura Tallafin Kudi na Kasa
(6) Mista Ayuba Gufwan — Babban Sakataren Hukumar Kula da Nakasassu ta Kasa
(7) Lami Binta Adamu Bello — Darakta Janar ta Hukumar Hana Fataucin Bil Adama ta Kasa.
A sanarwar da Mai baiwa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai, Ajure Ngelale ya fitar a jiya Talata, Tinubu ya hore su da su rike ma’aikatun da aka basu da amana domin tabbatar da cewa ƴan Nijeriya, musamman marasa galihu sun amfana da irin kashi-kashin tallafi da gwamnatin sa ta ɓullo da su.