Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zauren majalisar wakilai

Dukkan wasu shirye shirye sun gama kammala, na bayyanar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, a gaban zauren majalisun dokokin Najeriya, domin gabatar daftarin kasafin kuɗin shekarar 2018.

A ranar 2 ga watan Nuwamban nan ne dai shugaban ya aikewa da majalisar dattawa da ta wakilai wasika, yana mai sanar da su aniyarsa ta gabatar musu da daftarin kasafin kuɗin shekarar 2018 kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar.

Ana sa ran Shugaban Majalisar Dattawa Abubakar Bukola Saraki tare da Kakakin Majalisar Dokoki ta kasa Yakubu Dogara zasu tarbi shugaban kasa Muhammadu Buhari a gaban zauren majalisar domin gabatar da daftarin.

Da misalin karfe biyu na rana agogon Najeriya ne ake sa ran shugaban zai gabatar da daftarin kasafin kudin,kamar yadda ya sanar a cikin wasikar da ya aikewa zaurukan majalisun dokokin a yau talata.

DAILY NIGERIAN HAUSA ta shirya tsaf domin kawo muku cikakken rahoto.