
Hedikwatar tsaro ta ƙasa, DHQ, ta karyata rahoton da ke cewa shugaban hafsoshin tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya mutu.
Da safiyar yau Talata ne wasu jaridu suka buga wani rahoto na cewa Musa ya mutu.
Amma a wani martani na gaggawa da DHQ ta yi a cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na X, ta bayyana cewa Babban Hafsan Tsaro yana raye kuma cikin koshin lafiya.
Ta bayyana rahoton a matsayin karya, tana mai kara da cewa babban hafsan hafsoshin tsaron na cikin koshin lafiya.
Ta kara da cewa “A dogara da majiyoyi masu inganci don samun ingantattun bayanai.”
Shugaban kasa Bola Tinubu ne ya nada Janar Musa a matsayin babban hafsan tsaro a ranar 19 ga watan Yunin 2023.