Home Labarai Shugaban Kasar Amurka ya ci alwashin soke TikTok a ƙasar

Shugaban Kasar Amurka ya ci alwashin soke TikTok a ƙasar

0
Shugaban Kasar Amurka ya ci alwashin soke TikTok a ƙasar

Shugaban Kasar Amurka, Joe Biden ya ce zai rattaba hannu kan dokar da za ta soke amfani da manhajar TikTok a ƙasar.

A cewar Skynews, an zartar da kudirin dokar ƙarƙashin Kwamitin Makamashi da Kasuwanci na Majalisar Dokokin Amurka gaba daya a ranar alhamis din da ta gabata, suna kira ga kamfanin ByteDance na kasar China da ya karbe ikon mallakar TikTok ko kuma ya fuskanci kora a Amurka.

Kakakin majalisar wakilai ta Republican, Mike Johnson, wanda ya dauki nauyin kudirin, ya nuna cewa nan ba da jimawa ba za a kada kuri’a a majalisar.

“Idan sun zartar, zan sanya hannu,” in ji Biden lokacin da manema labarai suka tambaye shi game da dokar.

Fadar White House ta kafa kwamitin kwararru wajen tsara kudirin, amma jami’in yada labaran fadar White House, Karine Jean Pierre ta ce a farkon wannan makon dokar TikTok “har yanzu tana bukatar wani aiki” don isa wurin da Biden zai rattaba hannu.

Tsohon shugaban kasar Donald Trump, mai shirin zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican, ya wallafa a shafinsa na True Social a ranar Alhamis yana mai nuna rashin amincewarsa na soke TikTok ne saboda zai taimaka wajen adawa da dandalin sada zumunta na Facebook.

A baya Trump din ya ba da umarnin soke TikTok da WeChat, daga bisani kuma ya janye a ƙarshen wa’adin mulkin sa.