Daga Hassan Y.A. Malik

Rundunar sojojin bataliya ta 93, a jiya Lahadi ta cafke wani wanda a ke zargi da cewa dan leken asirin masu kashe-kashe ne, a yayin da ya ke kokarin binciko bayanai akan wani wanda za su kashe.

Dan leken asirin na fakon wanda suke harin ne a yayin da ya ke tafiya a mota a kan hanyar Takum zuwa Chanchangi a jihar Taraba a lokacin da sojojin suka kama shi.

A wata sanarwa da daraktan yada labarai na sojin Nijeriya, Birgediya Texas Chukwu, ya fitar ya bayyana cewa, wani mutum mai tafiyar kafa ne ne ya ji lokacin da shi  dan leken asirin ke magana da wani Malam Musa Ibrahim cewa ya shaida mutumin da za su kaddamarwa.

A lokacin da sojoji ke tuhumar wanda ake zargin, ya tabbatar da cewa shi dan leken asiri ne da ke yi wa masu aikata muggan laifuka aikin leken asiri.

A yanzu haka dai wanda a ke zargin na hannun sojoji kuma suna ci gaba da tuhumarsa don samun wasu bayanan.