34.1 C
Abuja
Friday, April 19, 2024

Sojojin Kamaru na gallazawa ‘yan Najeriya

Must read

Jaafar Jaafar
Jaafar Jaafarhttps://dailynigerian.com/
Jaafar Jaafar is a graduate of Mass Communication from Bayero University, Kano. He was a reporter at Daily Trust, an assistant editor at Premium Times and now the editor-in-chief of Daily Nigerian.

A wani rahoto da gidan radiyon BBC Hausa ya wallafa a shafinsa na intanet, sun bayyana yadda kungiyar kare hakkin bil dama ta zargi sojojin kamaru da gallazawa ‘yan gudun hijirar Najeriya dake kamarun. Kungiyar ta kuma sanya Kamaru cikin jerin wasu kasashen duniya da ta ce sun yi kaurin suna wajen tursasawa ‘yan gudun hijira komawa kasashensu.

Ta bayyana hakan ne yayin kaddamar da wani rahoton da ta fitar a kan hakan a ranar Laraba a Abuja.

Kungiyar ta kuma nuna damuwa game da rawar da ta ce Najeriya ta taka wajen mayar da wasu ‘yan gudun hijirar gida.

Human Rights Watch na zargin sojojin Kamaru cewa suna taso keyar ‘yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu, da cin zarafin su da cuma keta musu haddi.

”Kamaru na hukunta ‘yan gudun hijira saboda hare-haren da ‘yan Boko Haran suka kai kasar,” in ji kungiyar.

Kamaru ta musanta zargin da aka mata a baya, inda ta ce ‘yan Najeriyar suna komawa gida ne bisa son ransu.

Wani rahoto na HRW din ya ce: ”Tun farkon shekarar 2015, hukumomin Kamarun sun tursasawa ‘yan Najeriya fiye da 100,000 komawa gida inda yaki bai sarara ba. wadanda a da suke zama a wasu yankuna da ke kan iyakar kasar da Najeriya.”

”Garin fitar da ‘yan Najeriya daga kasarsu, sojojin Kameru su kan dauki matakan cin zarafi da suka hada da duka.

Wani mutum dan shekara 43 daga jihar Borno ya fadawa HRW cewa dan uwansa ya mutu sakamakon raunin zubar jini da yawa da ya yi, bayan sojojin Kamaru sun masa dan banzan duka da sanda.

Ya ce: ”Sun azabtar da mu kamar dabbobi kuma sun mana duka kaman bayinsu.”

A farkon wannan shekaran, hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta soki Kamaru da tursasawa daruruwan ‘yan gudun hijirar Najeriya komawa arewa maso gabashin Najeriyar.

Hukumomin Kamaru dai sun ce mayakan Boko Haram suna yin badda kama ne su shiga kasar a matsayin ‘yan gudun hijira.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce, tursasawa ‘yan gudun hijira su koma gida kamar keta dokokin hukumar ne.

Hukumar UNHCR ta ce tursasawar da Kamaru ke yi ga ‘yan gudun hijira su bar kasar mummunan karan tsaye ne ga yarjejeniyar hukumar wadda aka cimma a shekarar 1951 da kuma ta kungiyar Tarayyar Afirka da aka cimma a 1969, wadanda duk Kamaru ta sa hannu wajen amincewa da su.

A can baya dai hukumar ta yi kira ga Kamaru ta girmama yarjejeniyar ta kuma bar kan iyakokinta a bude don masu neman mafaka da ke gujewa rikicin Boko Haram su shiga.

Tun da farko an yi kira Kamaru don ta cika alkawarinta a karkashin yarjejeniyar kuma su ci gaba da ba da izinin shiga yankin da hanyoyin mafaka ga mutanen da ke gudun hijira daga Boko Haram .

More articles

Latest article