Home Labarai Sojojin sama sun hallaka ƙasurgumin ɗan ta’adda, Yellow Jambros a Neja

Sojojin sama sun hallaka ƙasurgumin ɗan ta’adda, Yellow Jambros a Neja

0
Sojojin sama sun hallaka ƙasurgumin ɗan ta’adda, Yellow Jambros a Neja

Rundunar sojin sama na ‘Operation Whirl’ ta yi nasarar kashe wani fitinannen dan ta’adda da garkuwa da mutane, Yellow Jambros, da wasu da dama daga cikin ‘yan ta’adda a wani harin jirgin sama da ta kai a karamar hukumar Shiroro, ta jihar Neja.

Rundunar sojin saman Najeriya, NAF ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da daraktan hulda da jama’a da yada labarai, Air Commodore Edward Gabkwet, ya fitar a yau Lahadi a Abuja.

Gabkwet ya ce ‘yan ta’addan sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suke yunkurin tsallakawa kogin Jikudna da ke gundumar Galadima Kogo, inda suka nufi Wurukuvhi a karamar hukumar Chikun.

Ya ce an bi sahun Yellow Jambros tare da tawagarsa tun daga daga Zamfara zuwa Neja, lokacin da suke tafe a kan babura guda 13 a kan iyakar jihar Kaduna da Nijar, inda suka nufi Kusasu a Shiroro, kafin a kai musu harin ta sama.

“A Kusasu, wasu ƴan ta’adda guda biyar da suke tuka babur sun shiga ayarin motocin Yellow Jambros, inda adadin baburan ya kai 18, daga nan suka nufi gabar kogin Jikudna.

“A bakin kogin, ‘yan ta’addan da babura 18 sun shiga wani katon kwale-kwale mai amfani da lantarki a kokarinsu na tsallakawa da sauran ‘yan ta’adda a fadin kogin.

“A wannan lokacin ne aka ba da izinin gudanar da yi musu luguden wuta,” in ji shi.