Kalaman Maigirma Gwamnan jihar kebbi Sen Abubakar Atiku Bagudu kenan a kasuwar Birnin Kebbi lokacin da ya ke zantawa da shugaban kasuwar Malam Umar Dangura, jiya Assabar 13/04/2019 akan Ibtila’in da ya faru na gobara a kasuwar kwanaki biyu da suka gabata, har ta yi sanadiyar konewar shaguna Bakwai ciki har da dukiya.

Shugaban Kasuwar ya fadawa Gwamnan cewa tabbas sun Kira hukumar kashe Gobara, kuma sun zo da Motocin su na kashe Gobara. Hukumar ta yi kokari Sosai Allah ya sa wutar ta tsaya bakin shagunan da watar ta fara tashi.

Bayan Haka Maigirma Gwamnan jihar kebbi ya Jajanta tare da tausayawa kan hasarar da aka yi.

Kuma Gwamnan ya yi Kira ga masu rubuce-rubuce kan rashin motocin kashe Gobara mallakar Gwamnatin Jiha da su dinga bincike kar su fadi abin da ba haka ba, domin akwai Motocin kashe Gobara cikin Hedikwatar babban birnin jihar (Birnin kebbi) guda Biyar, Hudu mallakar Gwamnatin jihar kebbi ne. Kuma da su ne aka yi kokarin takaita wutar.

13/04/2019.