Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osibanjo tare da 'yan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Super eagles a lokacin da suka kai masa ziyara a fadar Gwamnati dake Aso Villa a Abuja

Kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Super eagles sun sha alwashin ciwo kofin duniya da za’a buga a Rasha 2018. Kungiyar ta bayyana hakan ne a lokacin da ta kaiwa Shugaban kasa Muhammadu Buhari caffa a fadarsa dake Abuja, yayin da suka je domin neman a sanya musu albarka kafin tafiyarsu zuwa kasar Rasha.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da mataimakinsa Yemi Osbanjo ne suka tarbi tawagar ‘yan wasa, a yayin da suka kai ziyara fadar ta Shugaban kasa. Da yake jawabi Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi musu fatan alheri da kuma fatan zasu ciwo wa najeriya kofin duniya a yayin gasar.

Suma a nasu jawabin,’yan wasan sun nuna jin dadinsu da kuma bayyana cewar zasu yi duk abinda zasu yi wajen ganin sun ciwowa Najeriya wannan gasa ta cin kofin duniya a kasar Rasha.