
Sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta Kudu a zauren majalisar, Sunday Marshall Katung, ya ce zai yi aiki tare da sauran ‘yan majalisar tarayya daga jihar domin tabbatar da cewa an bi hakkin wadanda harin bam da sojoji suka kai wa wata al’ummar Kaduna.
Rundunar sojin Najeriya a ranar Litinin din da ta gabata ta dauki alhakin harin da dakarunta ta kaiwa wasu mutane suna tsaka da yin Maulidi a kauyen Tudun Biri da ke gundumar Afaka a karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna, inda ta ce bisa kuskure ne.
A wata sanarwa da ya fitar domin jajantawa al’ummar jihar Kaduna da al’ummar da abin ya shafa, Sanata Katung ya ce za su tabbatar da kula da wadanda suka tsira.
“Wannan lamarin wani abin takaici ne da kuma koma baya ga sabbin hare-haren da ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga ke kaiwa a yankin, jihar Kaduna da ma kasa baki daya,” in ji shi.