Home Siyasa Ni ɗan takara ne don Nijeriya ba Igbo ba — Obi

Ni ɗan takara ne don Nijeriya ba Igbo ba — Obi

0
Ni ɗan takara ne don Nijeriya ba Igbo ba — Obi

 

Dan takarar shugaban kasa a Najeriya na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya ce shi yana takara ne don ƴan Nijeriya baki ɗaya ba wai don ƴan ɓangaren inyamirai ba.

Ya fadi haka ne a wata hira da jaridar Daily Trust, inda ya ce idan ya ci zaɓe a 2023, zai yi wa gaba ɗaya Nijeriya aiki ne ba ɓangaren ƴan uwansa inyamirai ba.

Ya kuma ce zai tattauna da ‘yan haramtacciyar kungiyar nan ta masu fafutukar neman ‘yancin Biafra (IPOB) da sauran masu fafutuka domin maido da zaman lafiya kasar, idan aka zabe shi.

Dan takarar na jam’iyyar Labour wanda tsohon gwamnan Jihar Anambra ne, ya ce salonsa zai zama daban da na takwarorinsa kan wannan matsala idan har aka zabe shi a ranar 25 ga watan Fabrairu na shekara mai kamawa 2023.

Obi ya ce, ya sha nanatawa ba sau daya ba ba sau biyu ba, cewa Najeriya ba ta da masu fafutuka fiye da kasar Brazil.

”Idan kana so zan nuna maka kasashen da suka yi fama da masu fafutuk a baya, ko Brazil ce ko Mexico ce, ko wannan ce.

”A kudu maso gabashinmu abu ne mai sauki, zan yi tattauna, zan tattauna, dumukuradiyya ce kuma a mulkin dumukuradiyya kana mulki ne da cimma matsaya. Idan wani ya ce ba ya jin dadi, sai ka kira shi ka zauna da shi ka tattauna da shi,” in ji Mista Obi.