Home Siyasa Ɗan takarar gwamna a PDP ya nemi a dawo masa da N21m ɗinsa da ya sayi fom

Ɗan takarar gwamna a PDP ya nemi a dawo masa da N21m ɗinsa da ya sayi fom

0
Ɗan takarar gwamna a PDP ya nemi a dawo masa da N21m ɗinsa da ya sayi fom

 

 

 

 

Wani ɗan jam’iyyar PDP, Wilfred Bonse, ya janye daga takarar gwamna a Jihar Cross River a zaɓen 2023, inda ya nemi jam’iyyar ta mayar masa da naira miliyan 21 da ya sayi fom.

 

Bonse, a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN a Abuja a jiya Talata, ya danganta neman dawo masa da kuɗin nasa ​​da “rashin adalci” daga jam’iyyar na hana shi shiga zaɓen fidda-gwani na gwamna da za a yi a Cross River.

 

Sai dai kuma a cewar wani jami’in jam’iyyar, ba a dawo da ƙudaden fom ɗin takara da ɗan takara ya rigaya ya saya.

 

Amma kuma, a cewar Bonse, jam’iyyar ta ƙi amincewa da soke shi daga sunayen ƴan takarar, ko ta amince masa ya tsaya takarar har ya shiga zaɓen fidda-gwani na jam’iyyar da za a yi ranar Laraba.

 

“Ina rokon jam’iyya da ta dawo mini da  Naira miliyan 21 da na biya na sayen fom ɗin takarar.

 

“Idan da alal misali, an ba ni dama mai kyau na shiga zaɓen fidda-gwani, kuma na yi rashin nasara, ba zan damu ba. Amma kawai sai a riƙa tare ni ana toshe ni a kowanne mataki.

 

“Wani mamban kwamitin amintattu (BOT) ya baiwa jam’iyyar PDP takarda, inda ya bukaci su sake duba lamarina domin kada jam’iyyar ta fadi zaben gwamna a jihar bisa la’akari da asali da tarihi na.

 

“Amma sun ƙi jin abinda ya faɗa kuma ga lokacin ya matso daf da daf. Kamar yadda nake magana, muna da kasa da kwanaki bakwai zuwa ga zaɓen fidda-gwani.

 

“Sabuwar dokar zabe ta tanadi cewa za a yi kwanaki bakwai ana tantance ƴan takara, kafin zaben fidda gwani da kuma aika sunana ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC).