Daga Hassan Y.A. Malik

Tsananin talauci ya sanya mazaje baiwa turawa hayar matansu na dan wani lokaci domin su samu kudin da za su kula da iyalansu.

Wannan kwamacala dai na faruwa ne a kauyen Kwale da ke Mumbasa a kasar Kenya inda a kowacce shekara dubunnan turawa ke zuwa yawon bude ido

Lamarin ba ya tsaya ne akan maza ba kawai, har mata ma na bada hayar mazajensu ga matan turawa na wani lokaci.

Wasu ma’aurata a kauyen na Kwale da aka bayyana sunayensu da Sande Ramadan da matarsa Wambui, sana’ar da suke yi kenan domin su kula da ‘ya’yansu uku.

A wani rahoto da Aljazeera ta wallafa, Sande wanda ke tare da matarsa na tsahon shekaru 20 ya bayyana cewa sun fara wannan harka ne a 2006.

Ya ce a lokacin ya na sayar da riguna ga turawan da ke zuwa yawon bude ido kauyensu, kuma a ko da yaushe a cikin babu suke saboda kudaden da ya ke samu ba su isa ya kula da iyalansa.