Home Ƙasashen waje Taliban ta cafke mutumin da ya sayar da mata 130 a Afghanistan

Taliban ta cafke mutumin da ya sayar da mata 130 a Afghanistan

0
Taliban ta cafke mutumin da ya sayar da mata 130 a Afghanistan

 

Taliban ta cafke wani mutum da zargin yaudarar mata 130 kan cewa za a yi musu hanyar aurar masu kuɗi a arewacin Afghanistan.

An kama mutumin ne a arewacin Jawzjan a ranar Litinin inji shugaban ƴan-sandan Taliban, Damullah Seraj.

Seraj ya ce mutumin yana yaudarar matan ne a zuwan zai samar musu kazan aure masu kuɗi amma karshe sai ya je ya saida su su riƙa yin bauta.

Ya ƙara da cewa za a hukunta mutumin dai dai da yadda doka ta tanada.