Bikin nadin sarautar Sarkin Zazzau Alu dan Sidi a ranar 27 ga watan Yunin shekarar 1903

Daga Dandalin Tarihin Magabata

Sarkin Zazzau Aliyu Dan Sidi shahararren basarake ne a Arewacin Najeriya. Ya yi fice saboda irin fasaharsa da illiminsa, kuma shine sarkin Zazzau na farko da Turawa suka nada.

Turawanne kuma suka sauke shi, bayan sun samu sabanin ra’ayi akan wasu sauye-sauyen zamani. Ya zama sarki yana da shekaru 64. Ya yi sarautar Zazzau daga shekarar 1903 zuwa 1920.

Jikan Sarkin Zazzau Musa ne, Bamalli. Wani abin sha’awa game da da tarihinsa shi ne, shi dai bai taso a gidan Sarautar Zazzau ba, ya taso a gidan malanta ne, a hannun malaminsa Limamin Durum wato Malam Abubakar.

Ya taba samun sabani da Sarkin Zazzau Kwasau (Mai kogin Jini dan Sambo), wanda hakan ya sanya ya bar Kasar Zazzau, ya shiga yawace-yawace, inda har ya zauna a kasar Kwantagora a zamanin Sarkin Kwantagora Ibrahim Nagwamatse.

Ya wallafa wakoki da dama, cikinsu kuwa akwai Tabarkoko, Saudul Kulubi, Wakar Diga da kuma wakar Birnin Kano.

An ce wakar Birnin Kano ya yita ne, yayin wata dabar bankwana da sarakunan Arewacin Najeriya su ka shiryawa Gwamna Arewacin na Zamanin Turawa wato Sir Hugh Clifford, a Birnin na Kano a cikin shekara 1914. A zamaninsa akan masa kirari da “Aliyu na Awwa mai iya Sarki”.

Sarkin Zazzau Aliyu dan Sidi Batijjane ne na kwarai, kuma ya yiwa shehin Darikar ta Tijjaniya wato Shehu Ahmadu Tijjani waka.

Wakar Birnin Kano ta Malam Alu dan Sidi

Muna gode Allah da yayi nufi

Yasa muka taru a kofar Kano

Muna yin Salati bisa ga Muhammad

Dalilinsa anka yi mu akayi Kano

Mu kara salati bisa ga sahabbai

Mu sami dalilinsu komi anu

Zama hali ma nahnu shi muka zance

Da niy yi shiri zani birnin Kano

Diya min Muharram ga ran Lahadi

Na hau bisa jirgi zuwa na Kano

Ga Chalawa ni kwana guda muka tashi

Muna gaisuwa da dawakan Kano

Dawaki na baki kaza yan gari

Fa har muka sadu da Sarkin Kano

Da fa muka gaisa ya juya na bishi

Dada har ya kaini masauki Kano

Ina gaida masu zuwa daga nesa

Da shaihu na Kukawa ga shi Kano

Da Mahoni Laraba Gaidan Kano

Kaza Lamido Adamawa a birnin Kano

Katagum, Hadejia, kaza duk da Gombe

Misau Jama’are a birnin Kano

Da Zazzau da Bauchi, kaza Katsina

Da Daura, Gumel gasu birnin Kano

Kazaure da kau Sakkwato har da Gwandu

Kabawa da Argungu birnin Kano

Mutan Gwadabawa da Kwanni da Yabo

Gamuwa da Anka a birnin Kano

Da Meri da Augi mutanen Yamma

Mutan Jega ga su a birnin Kano

Mutan Wukari, mutanen Ibi

Da Loko da Lokoja a birnin Kano

Da Yawuri har Kwantagora Rijau

Mutan Wushishi da Bussa a Birnin Kano

Kushurki da Kunguna har Kuriga

da Gwari na Waki a taron Kano

Mutanen Maginga mtan Kanbuwa

Na Sulame gasu a birnin Kano

Illori, Nufawa, Lafai, Agaye

Fa hatta Abuja a birnin Kano

Fa har Tunkiya gata ga Damisa

Mashayansu dai sunyi kiwo Kano

Kutawa mutanen Kafi, Lafiya

Da jam’an ta Baroro a birnin Kano

Da Mahmudu Ningi da Sarkin Bura

Da Sarkin na Bassa a birnin Kano

Ina gaida Sarkin Kano Yayi Aiki

da anka yi taro garinsa Kano

Gidaje na sabka dada har liyafa

Da taryan sarakai su sabka Kano

Da sabkan farare da sabkan bakake

da birni da kauye a birnin Kano

dalili gareni in san yayi aiki

Zama nayi ko da nika je Kano

Da shi da ya sabkar da su masu sabka

Ta’ala shi bamu sawaba Kano

Fa naje da yare iri da yawa

Da busa da ganga a taron Kano

Fitawa da doki dako Feluwa

Da sayi suna sukuwa nan Kano

Mutane da doki da niz zo dasu

jimillansu hamsa zuwana Kano

Kurama, Katab har da Cawai duka

Fa duk sunyi wasa a taron Kano

Da Jaba da Gwari mutan Rumaya

Kadara fa na kai su taron Kano

Ga babban suka na dawakan saraki

Na Zazzau fa sun ka ci taron Kano

Da anka yi wasa fage ya hadu

Muhudanmu sun yi ado nan Kano

Ka rarra, ka Kabra, ku san tumkiya

Bata iya kabra ba Kano

Da tauri da tsauri idan anka goga

Guda sai shi yanke guda a Kano

Ba’an gwada karfe ba, sai inda karfe

Duwatsu fashewa su kai a Kano

Ka zaga Kano har kasan dan Kano

Na birnin Kano wanda yasan Kano

Ka kau tambaye shi tsakani da Allah

Ya bayyana maka taron Kano

Na yawata Kano gani ga dan Kano

Dada har nasan anguwa a Kano

akwai anguwan madawkin Kano

Da sunanta Yola a birnin Kano

Daneji, da Soron dinki akwai su

akwai Lungunawa da Sheshe Kano

Da Marmara duk unguwa ce duka

da Kunduke Kwankwaso duk a Kano

Akwai Wudilawa akwai Na’ibawa

Da Ibadi Fasa-keya a birnin Kano.

Caranci, Gudundi, akkwai Jarkasa

Makankari, Garko duk a Kano

Kusura, Kudancin Kano da Wazirci

Da Siradi akwai ta Kano

Karofi na Wanka da Shuni akwaisu

Madatai da Daushi akwai su Kano

Karofi na Sudawa, Zangon Ciki

Da Dandago, Diso akwai su Kano

Akwai unguwar Durunmin Kaigama

Da Bulbulas, Guntu akwai su Kano

Da Yalwa da Dala, Madaboo duka

Suna nan Arewa da Kurmin Kano

Akwai wata ko unguwa Masaka

Da Sarari da Sagagi Birnin Kano

Awai unguwa Waitaka a Kano

Akwai Durumin Dakata min Kano

Mahanga, Kutumbawa duk unguwa ce

Da Damtsenka Tsage a Birnin Kano

Akwai Cediya ta Kuda unguwa ce

Akwai Kalaman Dusu duk a Kano

Da Lallokin Lemu, da kau Makwarari

Makwalla fa duk unguwa ce Kano

Dabinon Awansu da Mandawari

Da Alfindiki Kwalwa duk a Kano

Tsaya in gajarta guda don kau yawaita

In kawo wurinta da niyyi Kano

Fa har muka kare naje Nasarawa

Garin makarantan su Sambon Kano

Akwai makaranta karatun Bature

Acan Nasarawa ta kofar Kano

akwai yara masu Karatu na allo

Akwai masallaci ginanne Kano

AKwai Makaranta ta al Kur’ani

Da litattafanmu a birnin Kano

Akwai wani dakin zaman masu ciwo

Akwai matsarinsu a kofan Kano

Masaka, madunka, da mai Sassaka

Gidansu guda makarantan Kano

Makera, Badukai da masu kudi

Cikin makaranta ta kofar Kano

Cikin shekara goma sha dai ga daula

Aliyu binu Sidi zuwanshi Kano

Ya wake ta yan baya domin su ji

Su san wakacin tafiyanshi Kano.

 

Allah Ya Gafarta Masa