Marigayi Malam Abubakar Atiku Sanka

Daga Malam Fatuhu Mustapha

Cikakken sunansa shine: Abubakar Atik bin Khidr bin Abubakar bin Musa Mai Risala, al Kashnawi, al Kanawi al Tijjani.

Asalinsu mutanen Katsina ne, Malam Musa Mairisala ya baro Katsina a zamanin jihadi, ya dawo Kano, ya zauna a Kabara, inda ya kafa makaranta, cikin daliban da suka yi karatu a gabansa, har da Sarkin Kano Dabo, a lokacin yana ladanci a masallacin Sarkin Dawaki Maituta.

Kakansa Malam Abubakar shine ya koma Sanka ya gina gidansa, inda aka haifi Shehu Atiku Sanka a shekarar 1911.

Shehu Atiku ya taso a hannun kakarsa ta wurin uwa, wadda ake kira Rahma bint Abdulmalik, an haifeta a shekarar 1860. A hannun mijinta  Ismail bin Muhammad, wanda aka fi sani da Malam Abba, ya fara karatu. A wurinsa ya sauke Alkurani, kuma ya karanci litattafai irinsu Lahallari, Mukhtasar, Manzuma ta Kurdabi, Burda ta Busiri da kuma Tahamisin Badamasi.

Daga nan sai ya koma almajirci a wurin Sheikh Muhammad Salga, inda yayi karatun Fikihu, da Tawhidi. A Fikihu ya karanci litattafai irinsu Risala ta Abi Zaid, Irshad al Salik ta Ibn Askar da Muqaddima ta ibn Rushd.

A bangaren Tauhidi kuma ya karanci litattatafai irinsu: Aka’id na al Sunusi, Dalilil Akaid na Al Awajali, al Manhal al Adab na Muhammad al Wali da Ida’atal Dujunna na Ahmad al Makari.

Ya tafi hajjin farko tare da babban abokinsa kuma malaminsa Abdullahi Mahmud Salga a 1951, inda bayan dawowarsa ya karanci lugga a wurin Malam Mahmud Hassan, da kuma Nazm al Kubra wallafar Tahir ibn Ibrahim al Barnawi.

Babban malaminsa na sufanci shine: malam Abubakar Mijinyawa. A wurinsa ya karanci Hikam na Ibn Ata Allah, da al Mabahith na al Banna, kuma a wurinsa ya karbi dariqar Tijjaniyya.

Duk da yake malam Mahmud Salga ne ya fara nada shi mukaddami, bisa shawarar da Sheikha al Karia ta bayar akan cancantarsa, a wata ziyara da ta kawo Kano a 1934. Ya kuma samu wasu ijazar daga: Muhammad al Alami, da kuma Mulay Muhammad al Timbukhti. Da Sharif Said bin Umar da Sheikh Niase, da Sheikh Hadi bin Maulud al Fal da sauransu. Har ma ya rubuta al Khulasat al Ijaza, domin ya bayyana isnadin ijazarsa.

Ya rubuta litattafai da dama, ga wasu daga ciki:

1) Majmu’i mai kundi 14, da aka hade kananan ayyukansa irinsu Ifadat al Murid, Futuhatul Mannan, Raf al I’itirad, al Fuyudat da sauransu.

2) Abyatul Rakika, akan murnar ziyarar da malaminsa al Hajj bin Umar ya kawo Kano.

3) Asl Ammani akan mata muqaddimai

4) Badhl Nada akan kasidar Ishiriniya

5) Fathal Ahad akan wadanda suka yi shahada a yakin Uhud

6) al Fathal nurani akan wuridin Tijjaniyya

7) al Faydal Ahami akan tarihin manyan malaman dariqar Tijjaniyya

8) al Anat al Bulada akan koyan luggar larabci

9) Irsalat al A’inna akan tarihin sarakunan Katsina

10) Irshadal al Ahibba akan haramcin shan taba

11) Manahil al Rashd amsa ga wasu fatawoyi da akayi masa daga kasar Chad

12) al Sarim al Mashrafi wani raddi da yayiwa Shehi Malam Nasiru Kabara. Akan wani littafi na Malam Nasiru maisuna Nafhatil Nasiriyya

13 Tanbihan Nubaha akan ko za’a iya ganin Manzon Allah (SAW) a farke. Ya kawo hadisai da suka nuna hakan acikin wannan kasida

14) Aybatal Fukara qasidar Hausa akan Shehi Ahmad Tijjani

15) Munjiyat an Niswan akan matsayin mata a Musulunci

16 ) Raka Dua ita ma wakar Hausa ce akan yadda zaka koyi luggar larabci.

An tabbatar da Malam Atiku ya rubuta sama da litattafai sittin a rayuwarsa.

Ya rasu a ranar 1 ga watan Mayun shekarar 1974.

Allah ya jikansa ya yafe kurakuransa.