Marigayi Malam Mudi Sipikin
Daga Fatuhu Mustapha
Wata rana malam Mudi Spikin ya dawo gida kawai sai ya hangi kofar gidansa cike da mutane ana ta hayaniya.  Nan da nan ya karasa da sauri domin yaga me ke faruwa, isar sa ke da wuya , ya tambayi wani mutum dake wurin, “me ke faruwa ne!” Mutimin yace masa ai barawo aka  kama ya saci buhun hatsi a gidan nan. Malam Mudi yace “subhanalLahi!” A gidan nawa?! Jin cewa shine maigidan yasa aka bashi wuri. Mutane kowa rike da makami, wasu na a miko shi mu gama masa aiki, wasu na a bari a kirawo yandoka.
Malam Mudi na shiga soro, yace ina barawo, aka ce masa gashi. Sai ya kalli barawo, yace masa ( cikin fada), “kai yanzu haka mu kayi da kai? Na gaya maka nima buhu guda ne, ya rage min a gidan nan, kuma ina da iyali, kuma ma ai cewa nayi in kazo kayi sallama, kace a auna maka rabin buhu, sai kawai kazo ka sunkuci buhu guda!!” Nan kuwa malam Mudi bai taba ganin barawo ba.
Nan kuma jikin kowa yayi sanyi, wani makwabcinsa yace ma, malam Mudi, “dama kai ka aiko shi?” Wani kuma ya kalli barawo, yace masa “kai ai sai kayi bayani, amma da kayi shiru, ai da tuni min gama maka aiki”
Nan da nan malam Mudi ya saka aka kawo kwanon awo, ya farke buhun nan da ya rage masa, ya aunawa barawo kwana 2o. Ya kulle ya daurawa barawo aka, har zai wuce, sai ya sanya hannu a aljihu ya dauko anini biyu ya mika masa, yace masa ga wannan in kaje kayi cefane, kasan uwargida sai da dan abin masarufi.  (Sai kace ya taba saninsa).
Tun daga ranar barawon nan ya tuba da sata.
Kaico! Ko yau a Arewa zamu samu dattawa irinsu malam Mudi Spikin? Allah ya jikansa da gafara!!