Wani sashe na mutanan da ake siyarwa a matsayin bayi a kasar Libya

Tawagar Gwamnatin Najeriya,karkashin jagorancin babban ministan harkokin kasashen waje Geoffrey Onyeama ta bar Abuja a ranar laraba domin zuwa birnin Turabulus babban birnin kasar Libiya domin kubutarda ‘yan Najeriya dake cikin halin kangi a kasar.

Kakakin kungiyar hana yaki da fataucin mutane ta NAPTIP, Josiah Emerole ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja.

Mista Emerole ya bayyana cewar, tawagar tana karkashin jagorancin ministan harkokin kasashen waje na Najeriya G. Onyeame.

“Sauran ‘yan tawagar sun hada da, Darakta Janar na NAPTIP Julie Okah Donli da kuma Abike Dabri-Erewa wanda mai taimakawa Shugaban kasa ne na musamman akan ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje”

Tawagar ta bar birnin tarayya Abuja da misalin karfe 9:20 na safiyar laraba a jirgin rundunar sojan sama na Gwamnatin Najeriya mai lamba N5FGS.

Ya kara da cewar, tawagar zata gana da jami’an Gwamnati a Libiya, da kuma jami’an ofishi Jakadancin Najeriya dake kasar, da kuma manyan kungiyoyi masu bayar da agaji ga masu gudun hijira.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, ya ruwaito cewar, harkar bautar da ake sanya ‘yan Najeriya a Libiya ya sanya Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari daukar wannan mataki na tura wannan tawaga domin ganin an kwaso duk ‘yan najeriya dake tagayyare a Libiya.

Haka kuma, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dorawa ministan harkokinkasashen wajen alhakin ganin an kwasu dukkan ‘yan Najeriya dake zaune acan cikin kangin bauta tare da mayar da su garuruwansu na asali a Najeriya.